Tinubu, Gwamnoni da manyan jami’an gwamnati sun halarci ɗaurin auren ’ya’yan Barau

Shugaban Ƙasar wanda ya zama a matsayin Wakili da Waliyi ga ‘ya’yan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta hannun Shugaban Majalisar Wakilai.

Tinubu, Gwamnoni da manyan jami’an gwamnati sun halarci ɗaurin auren ’ya’yan Barau

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Shugaban Majalisar Wakilai, Rt Hon Tajuddeen Abbas, Gwamnoni, Sanatoci, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje sun kasance daga cikin manyan baƙi da suka halarci ɗaurin auren ‘ya’yan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Barau I Jibrin.

Ɗaurin auren ɗan Sanata Barau, Jibrin Barau I Jibrin (Abba) da Maryam Nasir Ado Bayero, ɗiyar tsohon Sarkin Bichi da Aisha Barau I. Jibrin da Injiniya Abubakar, ɗan Dakta Abdulmunaf Yunusa Sarina, shugaban rukunin Kamfanonin Azman, wanda aka gudanar a babban masallacin Ƙasa da ke Abuja, bayan sallar Juma’a.

Shugaban Ƙasar wanda ya zama a matsayin Wakili da Waliyi ga ‘ya’yan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta hannun Shugaban Majalisar Wakilai. Yayin da Ganduje ya zama Waliyi ga ɗiyar Bayero, tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Tanko Almakura, ya kasance Wakilin Abubakar, ɗan Dakta Abdulmunaf Sarina.

Manyan ‘yan siyasa daga sassan ƙasar nan ne suka halarci bikin ɗaurin auren da manyan ‘yan jam’iyyun siyasa da suka haɗa da gwamnoni da Sanatoci da Ministoci da ’yan kasuwa da shugabannin gargajiya da na addini.

Gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da shugaban ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman AbdulRazaƙ; Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah; Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda.

Gwamnan jihar Kogi Ahmed Usman Ododo da gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni da dai sauransu.

Limamin masallacin ƙasa Farfesa Ibrahim Maƙari ne ya jagoranci ɗaurin auren.

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu