Tinubu na da tsare-tsaren farfaɗo da martabar Najeriya —Abdulmumin Jibrin
Ɗan majalisar ya yi kiran ne lokacin zaman haɗin gwiwa na kwamitocin harkokin kasashen waje na majalisun tarayya yayin kare kasafin kudin ma’aikatar wanda ya jagoranta tare da shugaban kwamitin na Majalisar Dattawa, Sanata Abubakar Sani Bello a ranar Litinin.
![Tinubu na da tsare-tsaren farfaɗo da martabar Najeriya —Abdulmumin Jibrin Tinubu na da tsare-tsaren farfaɗo da martabar Najeriya —Abdulmumin Jibrin](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2023/12/WhatsApp-Image-2023-12-12-at-10.33.38.jpeg)
Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji a Kano, kuma shugaban Kwamitin Harkokin Kasashen Waje, ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ƙara kuɗaden da ya ware wa Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje domin cimma kyawawan ƙudurorin da yake da su na harkokin kasashen waje, musamman ɓangaren bunƙasa dimokuraɗiyya da ci gaba.
Ɗan majalisar ya yi kiran ne lokacin zaman haɗin gwiwa na kwamitocin harkokin kasashen waje na majalisun tarayya yayin kare kasafin kudin ma’aikatar wanda ya jagoranta tare da shugaban kwamitin na Majalisar Dattawa, Sanata Abubakar Sani Bello a ranar Litinin.
Kwamitocin dai sun bi diddigin kasafin kudin ma’aikatar na 2023, sannan suka tace tare da tsefe kasafinta na 2024.
A lokacin zaman, Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ya yi ƙarin haske a kan kasafin ma’aikatar na 2024 sannan ya yi bayani daki-daki kan manufofin Shugaban Kasa kan ƙasashen waje.
- Sojoji sun kashe dan ta’adda Ali Kachalla da kwamandojin Dogo Gide
- ’Yan Arewa a Majalisar Tarayya sun ba da gudummawar N395m
Sai dai kwamitin haɗin gwiwar ya ce bisa la’akari da waɗancan kyawawan manufofin na Shugaban Ƙasa, kasafin kuɗin da aka ware wa ma’aikatar a 2024 ya yi ƙaɗan wajen aiwatar da su.
Daga nan ne sai kwamitin ya bayar da shawarar ƙara wa ma’aikatar kuɗaɗe a kasafin, inda ya yi alkawarin tattaunawa da Shugaban Majalisar Dattijai da Kakakin Majalisar Wakilai da ma kwamitocin kasafin kuɗi na majalisun biyu, ko da hakan zai kai ga tattaunawa da Shugaban Ƙasa domin yi masa bayani a kan haka.