Tinubu na tattaunawa da shugabannin ECOWAS kan juyin mulkin Nijar

Ana tattaunawar ce a kan halin da Jamhuriyar Nijar ke ciki

Tinubu na tattaunawa da shugabannin ECOWAS kan juyin mulkin Nijar

Tinubu da wasu shugabannin ECOWAS

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, yanzu haka yana tattaunawa da Shugabannin kasashen yammacin Afirka a karkashin inuwa kungiyar ECOWAS a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Ana tattaunawar ce a karkashin jagorancin shi Tinubun, wanda shi ne shugaban kungiyar, a kan halin da ake cikin bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaban Nijar, Mohammed Bazoum a Larabar da ta gabata.

Kasashe da kungiyoyi irin su Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar hadin Kan Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) da daidaikun kasashe ne suka bi sahu wajen yin Allah wadai da abin da ke faruwa a kasar.

A ranar Juma’a ce dai Kwamandan masu tsaro Fadar Shugaban Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya ayyana kansa a matsayin sabon Shugaban Kasar.

Daga cikin shugabannin da ke halartar taron na dakin taro na fadarya zuwa lokacin hada wannan rahoton akwai shugaba Umaro Sissoco Embalo na Guinea-Bissau da Alassane Ouattara of Cote D’Ivoire da kuma Faure Gnassingbe na Togo.

Sauran sun hada da Macky Sall na Senegal da Patrice Talon na Jamhuriyar Benin da Nana Akufo-Addo na Ghana, yayin da shugabannin Cape Varde da Liberiya suka samu wakilcin Ministocin Harkokin Wajensu.

Sai dai Shugaban rikon kwarya na gwamnatin kasar Chadi, Mahamat Deby, ya shiga fadar, amma ya fice kafin a fara shi.

Tinubu ya yaba wa NNPCL kan fara aikin Matatar Warri

Masu son Abba ya tsaya da ƙafarsa za su cuce shi – Kwankwaso

Matatar Warri ta fara aiki bayan shekara 9

’Yan sara-suka sun yi wa tela kisan gilla a Jos