Tinubu Ne Shugaban Kasa Mai Jiran Gado —Adamu

Abdullahi Adamu ya ce yadda mutane suka yi a dafifi a gangamin yakin neman zaben Tinubu ya nuna farin jinin APC a wurin ’yan Najeriya

Tinubu Ne Shugaban Kasa Mai Jiran Gado —Adamu

Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bugi kirji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu, ne zai karbi mulki daga Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

Sanata Abdullahi Adamu, ya bugi kirgin cewa Tinubu zai gaji Buhari ne a lokacin gangamin yakin neman dan takarar na yankin Arewa maso Yamma, inda ya ce yadda mutane suka yi cikar kwari a wajen ya tabbatar da irin farin jinin Jam’iyyar APC a wurin ’yan Najeriya.

“Ina gabatar muku da shugaban kasa mai jiran gado kuma magajin Shugaba Buhari a 2023, wato Bola Tinubu.

“Idan Allah Ya kai mu ranar 25 ba watan Janairun 2023, ku fito kwanku da kwarkwata, ku zabi Jam’iyyar APC,” in ji shi ga mahalarta gangamin da aka gudanar a Kaduna ranar Talata.

Abdullahi Adamu ya kuma yaba wa magoya bayan Jam’iyyar APC daga jihohin Kano, Katsina, Sakkwato, Kebbi, Zamfara da Jigawa da suka yi dafifi wajen halartar taron a Kaduna.

Tunda farko a jawabinsa, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa yawan jama’ar da ta taru a taron yakin neman zaben dan na takarar shugaban kasa na APC ya zama izina ga sauran jam’iyyu.

Gabanin taron, a ranar Litinin, Tinubu ya je Birnin Gwari, yankin da ’yan bindiga suka kafa wa kahon zuka a Jihar Kaduna, inda ya jajanta wa al’ummar yankin, tare da ba wa wadanda hare-haren ’yan bindiga suka shafa tallafin Naira miliyan 50.

Ya kuma yi alkawarin gina madatsan ruwa na zamani domin magance matsalar karancin ruwa da suke fama da ita a yankin idan ya ci zabe.

“Wadanda matsalar tsaro ta yi ajalinsu muna rokon Allah Ya sanya su a Aljannatul Firdausi,” in ji Tinubu a lokacin kai ziyara ga Fadar Sarkin Birnin Gwari, Malam Zubairu Jibril Maigwari.

Ya ci gaba da cewa, “[Idan na ci zabe] zan kawo muku zaman lafiya.

“Akwai wata sabuwar dama a nan gaba, zabe ya matso; ko ’yan bindiga sun sani, ko ba su sani ba, muna kara sanar da su cewa su tarkata komatsansu su yi gaba.

“Ba za mu sassauta ba a manufarmu ta kawar da ayyukansu da kuma kashe-kashe gaba daya a Najeriya.

“Ina tabbatar muku cewa wannan shi ne abin da za mu fi ba wa muhimmanci.”