Tinubu ne ya sauya ra’ayi kan ba ni muƙamin Minista — El-Rufai
A ƙarshe mun ƙulla yarjejeniyar cewa zai ba ni muƙamin Minista amma daga baya ya sauya ra’ayi.

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai
Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya musanta batun cewa Majalisar Tarayya ce ta ƙi tabbatar da shi domin zama Minista a shekarar 2023.
El-Rufai ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ne ya sauya ra’ayi kan ba shi muƙamin duk da sun ƙulla yarjejeniya a kan hakan.
- Uwa ta jefo jaririnta daga saman bene mai hawa biyu
- An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina
Ana iya tuna cewa, a watan Agustan 2023 ne Majalisar Dattawa ta ƙi tabbatar da El-Rufai a matsayin Minista, inda ta bayyana dalilai da suka shafi tsaron ƙasa da Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS ta ba da shawara.
Sai dai a hirarsa da gidan Talabijin na Arise a ranar Litinin, El-Rufai ya ce duk ba wannan ba ne face Shugaba Tinubu ne ya sauya shawara kan ba shi muƙamin.
A cewarsa, Shugaba Tinubu ne ya sauya masa akalar ƙudirinsa bayan shafe shekaru takwas a matsayin Gwamnan Kaduna.
“Bayan shafe shekaru takwas a matsayin Gwamnan Kaduna, ina da wasu burace-burace da na ƙudirta amma Tinubu ya nemi na bayar da gudunmawa a gwamnatinsa.
“Bayan haka ne muka ƙulla yarjejeniyar da sharaɗin cewa zai ba ni muƙamin Minista, amma daga bisani ya sauya shawara.
“Saboda haka a daina yarda da cewa Majalisar Tarayya ce ta ƙi tabbatar da ni saboda ba haka abun yake ba.
“Shugaban ƙasar ne kawai ba ya buƙata ta a gwamnatinsa saboda ya sauya shawara amma ko ma dai mene ne ba abin da ya dame ni ba ne,” in ji El-Rufai.