Tinubu ya aika wa Buhari budaddiyar wasika

Ta tabbata cewa Buhari na kowa ne.

Tinubu ya aika wa Buhari budaddiyar wasika

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya aika wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari budaddiyar wasika mai cike da yabo da jinjina.

Tinubu ya yi wa Buhari godiya marar iyaka dangane da zaben fid-da gwani takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC da aka gudanar makonnin da suka gabata.

A cikin wasikar da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Mista Femi Adesina ya raba wa manema labarai a ranar 18 ga watan Yunin 2022, Tinubu ya bayyana Buhari a matsayin jagora na hakika, dan uwansa kuma aboki na gari.

A cikin doguwar wasikar mai cike da kambabawa, Tinubu ya ce Buhari ya ribaci sanin ya kamatansa da dattako wajen jagorantar Babban Taron APC na musamman, wanda ya kai an tsayar da shi a matsayin gwanin takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar.

Da yake ci gaba da mika godiya da sakon ban girma dangane da taya shi murnar samun nasara a zaben fid-da gwani da Shugaban Kasar ya yi, Tinubu ya ce ta tabbata Buhari na kowa ne kuma mutum ne da son zuciya ba ya tasiri a kansa wajen mu’amalantar jama’a.

Tinubu ya bayyana gamsuwarsa dangane da yadda a cewarsa Buhari ya tsaya tsaka-tsaki wajen bai wa dukkan wadanda suka nemi tikitin takara na jam’iyyar APC damar gwada sa’arsu ba tare da nuna wata wariya ko son kai ba.

“A yayin da dukkan manema takarar suka yi tsammanin cewa Buhari zai zabi magajinsa, sai ga shi ya bude kofa kowa ya gwada sa’arsa ba tare da cewa ga gwaninsa ba saboda dukkaninmu kowa nasa ne.

“Kai [Buhari] na kowa ne kuma ba kada wani gwani guda daya a cikin dukkan wadanda suka nemi takara,” a cewar Tinubu.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya