Tinubu ya naɗa Badaru Ministan Tsaron Najeriya
Ga cikakken jerin ma’aikatun da aka kowanne Minista
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya nada tsohon Gwamnan Jihar Jigawa a matsayin sabon Ministan Tsaro na Najeriya.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata takarda daga Fadar Shugaban Kasar ranar Laraba da ke dauke da jerin ma’aikatun da shugaban ya ba Ministoci 45 din da Majalisar Dattijai ta sahale masa ya nada.
Shugaban ya kuma nada Tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike a matsayin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, yayin da tsohon Gwamnan Filato, Simon Lalong ya zama Ministan Kwadago.
Ita kuwa Mariya Bunkure ta zama Ministar a Ma’aikatar Babban Birnin Tarayya, sai Atiku Bagudu da ya zama Ministan Kasafi da Tattalin Arziki.
Tahir Mamman – Ilimi
Yusuf Sununu – Karamin Ministan Ilimi
Nyesom Wike – Abuja
Mohammed Badaru – Tsaro
Bello Matawalle – Karamin Ministan Tsaro
Ahmed Dangiwa – Gidaje da Raya Birane
Abdullahi T. Gwarzo – Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane
Simon Lalong – Kwadago da Ayyuka
Hannatu Musawa – Al’adu
Atiku Bagudu – Kasafi da Tsara Tattalin Arziki
Mariya Mahmud – Karamar Ministar Abuja
Bello Goronyo – Karamin Ministan Ruwa
Abubakar Kyari – Noma da samar da Abinci
Yusuf M. Tuggar – Harkokin Waje
Sa’idu A. Alkali – Harkokin Cikin Gida
Ali Pate – Lafiya
Ibrahim Geidam – Harkokin ‘Yan Sanda
Maigari Ahmadu – Karamin Ministan Karafa
Shu’aibu Abubakar Audu – Karamin Ministan Karafa
Mohammed Idris – Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a
Lateef Fagbemi – Shari’a/Babban Lauyan Gwamnati
Imaan Suleiman Ibrahim – Karamar Ministar ‘Yan Sanda
Zephaniah Jisalo – Ayyuka na Musamman
Joseph Utsev – Ruwa da Tsafta
Aliyu Sabi Abdullahi – Karamin Ministan Gona da Samar da Abinci
Bosun Tuani – Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani
Ishak Salaco – Karamin Ministan Muhalli
Wale Edun – Kudi da Tattalin Arziki
Bunmi Tunji – Ruwa
Adedayo Adelabu – Lantarki
Tunji Alausa – Karamin Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a
Dele Alake – Ma’adinai
Lola Ade-John- Yawon Bude Ido
Adegboyega Oyetola – Sufuri
Doris Anite – Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari
Uche Nnaji – Kimiyya da Fasaha
Nkiruka Onyejeocha – Karamar Ministar Kwadago da Samar da Ayyukan Yi.
Uju Kennedy – Ministar Mata
David Umahi – Ayyuka
Festus Keyamo – Sufurin Jiragen Sama
Abubakar Momoh – Matasa
Betta Edu – Walwala da Yaki da Talauci
Ekperikpe Ekpo – Karamin Ministan Iskar Gas
Heineken Lokpobiri – Karamin Ministan Man Fetur
John Enoh – Wasanni
Majiyoyi daga Fadar Shugaban Kasa dai sun ce ba a kai ga sanya ranar rantsar da sababbin Ministocin ba, amma kwanan nan ake sa ran fara yi musu bita.