Tinubu ya ba da umarni a binciki Meta, X, AI da Google kan amfani da labaran Najeriya
FCCPC za ta binciki ko kamfanonin sun yi amfani da labaran Najeriya ba bisa ƙa’ida ba.
Shugaba Bola Tinubu ya umarci Hukumar Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kayayyaki (FCCPC), ta binciki manyan kamfanonin fasaha da suka haɗa da Meta, Google, X (Twitter) da fasahar AI.
Umarnin ya biyo bayan ƙorafin da Ƙungiyar Kafafen Yaɗa Labarai ta Najeriya (NPO) ta kai wa gwamnati.
- ‘Babu diyyar da za a biya ’yan Najeriya da suka bar kadarori a Afirka ta Kudu’
- Harin Rasha ya yi sanadin mutuwar dalibar Najeriya a Ukraine
Ƙungiyar, wadda ta haɗa da mamallaka jaridu, ’yan jarida, gidajen rediyo da talabijin da masu wallafa labarai ta intanet.
Ƙungiyar ta zargi kamfanonin da yin harkokin kasuwanci ba bisa adalci ba da kuma amfani da labaran kafafen yaɗa labarai na Najeriya ba tare da izini ko biyan haƙƙinsu ba.
Hukumar FCCPC ta ce za ta gudanar da bincike mai zaman kansa cikin adalci domin tantance ko kamfanonin sun karya dokokin gasa da kare haƙƙin masu amfani da kayayyaki na Najeriya.
Hukumar ta jaddada cewa fara binciken ba yana nufin an same su da laifi ba.
Binciken zai mayar da hankali kan zargin cewa kamfanonin sun naɗi bahanai ko sun yi amfani da labarai da sauran bayanan kafafen yaɗa labarai na Najeriya wajen horar da fasahar AI ba tare da izinin hukumomi ba.
Haka kuma hukumar za ta binciki ko an hana kafafen yaɗa labarai na cikin gida samun diyya kan amfani da abubuwan da suka samar.
Hukumar ta bayyana yadda a shekarar 2025 ta ci tarar Meta dala miliyan 220 saboda laifukan da suka shafi kare bayanan masu amfani da dandalinsu.
Sai dai kamfanin ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin.
FCCPC ta kwatanta da abin da ya faru a Afirka ta Kudu, inda Google ya amince da biyan kuɗi ga kafafen yaɗa labarai bayan gudanar da irin wannan bincike.