Harin Mauludi: Tinubu ya ba da umarni a yi cikakken bincike
Tinubu ya ba da umarnin cikakken bincike da kulawa ga wadanda suka samu raunuka a sanadiyyar harin jirgin soja kan masu Mauludi a Kaduna
Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarni a yi cikakken bincike kan kisan masu taron Mauludi kusan 90 da wani jirgin soja ya jefa wa bom a Jihar Kaduna.
A safiyar Talata shugaban kasar ya ba da umarnin a cikin sakon ta’aziyyarsa game da rasuwar mutanen da tsautsayin ya auka musu a yankin Tudun Biri, Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.
Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta dauki alhakin harin, wanda ta ce wani jirginta mara matuki ne ya kai wa fararen hular bisa kuskure a lokacin da yake aikin yaki da ’yan bindiga.
Da yake jajantawa wa iyalan wadana abin ya shafa da kuma Gwamnatin Kaduna, Shugaban Tinubu ya bayyana takaicinsa kan harin da aka kai wa masu taron Mauludin.
- An binne mutum 80 bayan harin jirgin soji kan masu Mauludi
- Jami’an DSS da masu gadi sun ba hamata iska
Don haka ya ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike lamarin, da kuma cikakkiyar kulawa ga wadanda suka samu raunuka a sanadiyyar harin.
Ya yi addu’ar Rahamar Allah ga mamatan, sannan ya roki jama’a da su kwantar da hankalinsu a yayin da hukumomi ke nazarin abin da ya faru.
Kiran na shugaban kasa na zuwa ne bayan makamancinsa da Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya yi na gudanar da bincike a kan lamarin, domin hana maimaituwar hakan.
Gwamnan ya bayyana cewa wadanda suka samu raunuka suna samun kulawa a Asibitin Koyarwa na Barau Dikko, daga aljihun gwamnatin jihar.