Tinubu ya ba da umarnin biyan malaman jami’a albashin watannin da suka yi yajin aiki

Gwamnatin Buhari ce ta rike musu albashin lokacin da suka yi yajin aikin

Tinubu ya ba da umarnin biyan malaman jami’a albashin watannin da suka yi yajin aiki

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ba da umarnin biyan malaman jami’an jami’o’i karkashin kungiyar ASUU albashinsu na watanni 8 da aka rike musu yayin yajin aikin bara.

Mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da maraicen Juma’a.

Ya ce Tinubu ya dauki matakin ne a karkashin shirinsa na yin yafiya da nuna tausayi.

Ajuri ya ce tun shuka umarci Ma’aikatar Ilimi da ta Kwadago da su yi aiki tare wajen aiwatar da umarnin, kodayake ya ce wannan shi ne zai zama karo na karshe da gwamnatin za ta janye dokar ga ASUU da sauran kungiyoyin da ke bangaren ilimi.

Sai dai ya ce umarnin biyan albashin na watanni hudu ne kawai daga cikin watanni takwas din da suke bi.

A bara ne dai ASUU ta yi yajin aiki tun daga ranar 14 ga watan Fabrairu har zuwa 17 ga watan Oktoban 2022.

Sai dai a lokacin, gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta dakatar musu da albashin watannin da suka yi yajin aiki na takwas, inda ta fito da dokar “Ba aiki, ba albashi”.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan

Tags