Tinubu ya ba Ganduje da Gawuna shugabanci a Hukumar Filayen Jirage da Bankin gidaje
Tinubu ya naɗa tsohon Mataimakin Gwamnan Kano a zamanin Ganduje, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin Shugaban Majalisar Amintattu na Bankin Gidaje ta Ƙasa (FMBN).
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje a matsayin Shugaban Majalisar Amintattu na Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN).
Tinubu a kuma naɗa tsohon Mataimakin Gwamnan Kano a zamanin Ganduje, kuma ɗan takarar Gwamnan APC a Jihar a zaɓen 2023, Nasiru Gawuna, a matsayin Shugaban Majalisar Amintattu na Bankin Gidaje ta Ƙasa (FMBN).
Karo na biyu ke nan da Tinubu ke ba wa Gawuna irin wannan muƙamin, inda da farko ya naɗa shi shugaban Majalisar Amintattu na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK).
Ganduje da Gawuna suna cikin jerin mutane 42 da shugaban ƙasan ya naɗa a irin wannan muƙamin, kamar yadda kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya sanar.
Sanarwar ta ce naɗe-naɗen sun fara aiki ne nan take, kuma Tinubu ya gargaɗi sabbin shugabannin Majalisar Amintattun da su guji yin katsalandan a ayyukan hukumomin da aka naɗa su.
Sauran waɗanda suka samu muƙaman sun hada da:
- Yusuf Hamisu Abubakar (Mai rago) (Kaduna) – Hukumar Kula da Lafiyar Teku (NIMASA).
- Hon. Hillard Eta Chairman (Kuros Riba) – Hukumar Kula da Masu yi wa Ƙasa Hidima.
- Cif D. J. Kekemeke, Chairman (Ondo) – Hukumar Gidan Waya.
- Hon. Musa Sarkin Adar, Chairman (Sakkwato) – Hukumar Kula da Albarkatun Ruwa na Cikin Gida.
- Farfesa Abdulkarim Kana Abubakar, (Nasarawa) – Hukumar Tayar Albarkatun Tama.
- Hon. Garba Datti Muhammad, Chairman (Kaduna) – Hukumar Kula da Lafiyar Muhalli ta Ƙasa.
- Mu’azu Bawa Rijau, Chairman (Neja) – Hukumar Kare Haɗarin Sinadarai.
- Hon. Durosimi Meseko, Chairman (Kogi) – Cibiyar Binciken Gini da Hanyoyi ta Kasa.
- Hajia Zainab A. Ibrahim, (Taraba) -Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe.
- Dakta Kayode Isiak Opeifa, Managing Director (Legas) – Hukumar Sufurin Jirgin Ƙasa.
- Farfesa Bolaji Akinyemi, Chairman (Lagos) – Cibiyar Harkokin Ƙasa da Ƙasa.
- Sanata Surajudeen Bashiru Ajibola (Osun) – Hukumar Raya Harkar Sukari.
- Sulaiman Argungu (Kebbi) – Hukumar Dillancin Wutar Lantarki.
- Sanata Magnus Abe, Chairman (Ribas) – Hukumar Kare Kwararowar Hamada.
- Barr. Festus Fuanter, Chairman (Filato) – Cibiyar Inganta Aikin Koyarwa
- Kwamred Mustapha Salihu, Chairman (Adamawa) – Hukumar Rajistar Malamai ta Ƙasa.
- Hon. Hamma Adama Ali Kumo, Chairman (Gombe) – Asusun Tallafin Koyon Sana’o’i.
- Amb. Abubakar Shehu Wurno, Chairman (Sakkwato) – Hukumar Kula da Albarkatun Kogin Sakkwato-Rima.
- Augustine Chukwu Umahi, (Ebonyi) – Asibitin Koyarwa na Aminu Kano.
- Injiniya abatunde Fakoyede, (Ekiti) – Hukumar Tallafi Karatu ta Ƙasa.
- Hon. Shola Olofin, Chairman (Ekiti) – Asusun Inshorar Kyautata Rayuwa.
- Alh. Bashir Usman Gumel, (Jigawa) – Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Yola.
- Dakta Ijeoma Arodiogbu, (Imo) – Jami’ar Tarayya ta David Umahi da ke Jihar Ebonyi.
- Cif Edward Omo-Erewa, (Edo) – Hukumar Kula da Yoyon Ɗanyen Mai.
- Hon. Ali Bukar Dalori, Chairman (Borno) – Asibitin Koyarwa na Jami’ar Nnamdi Azikiwe, Nnewi, Jihar Anambra.
- Isa Sadiq Achida, Chairman (Sakkwato) – Hukumar Bincike da Inganta Samar da Kayayyaki.
- Hon. Lawal M. Liman – Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.
- Dakta Abubakar Isa Maiha – Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Katsina.
- Dakta Mohammed Gusau Hassan (Zamfara) – Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Birnin Kudu.
- Aare (Hon.) Durotolu Oyebode Bankole, (Ogun) – Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Ado-Ekiti, Jihar Ekiti.
- Abdullahi Dayo Israel, (Legas) – Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Abeokuta.
- Dakta Mrs. Mary Alile Idele, (Edo) – Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Asaba.
- Nze Chidi Duru (OON), (Anambra) – Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Lokoja.
- Hon. Emma Eneukwu, (Enugu) – Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ake Owerri.
- Uguru Mathew Ofoke, (Ebonyi) – Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Umuahia.
- Barista Felix Chukwumenoye Morka, Chairman (Delta) – Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Yenagoa.
- Donatus Enyinnah Nwankpa, Chairman (Abia) – Cibiyar Kula da Fasahar Gwaje-gwaje ta Kasa.
- Cif Victor Tombari Giadom, Chairman (Ribas) – Cibiyar Tsare-tsaren Ilimi da Gudanarwa ta Ƙasa.
- Sanata Abubakar Maikafi, (Bauchi) – Cibiyar Kimiyya da Fasaha ta SHEDA.
- Sanata Tokunbo Afikuyomi, (Legas) Cibiyar Mallaka da Kuma Yaɗa Fasaha ta Kasa.
- Manjo-Janar Jubril Abdulmalik (Murabus) Sakataren Hukuma Shige da Fice da Gidajen Yarin.
- Raji, Kazeem Kolawole, (Oyo) Darakta-Janar na Cibiyar Ƙyanƙyashe Fasahohi ta Kasa.