Tinubu ya ba wadanda rikicin zabe ya shafa a Kaduna Naira miliyan 10
A ranar Litinin da ta gabata jagoran Jam’iyyar APC ta kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas Sanata Bola Ahmed Tinubu ya raba wa Musulmi da Kirista da rikicin bayan zaben shekarar 2011 ya shafa tallafin Naira miliyan 10. Wadanda suka amfana da tallafin kudin sun fito ne daga yankunan Musulmi da Kirista da ke Jihar […]
A ranar Litinin da ta gabata jagoran Jam’iyyar APC ta kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas Sanata Bola Ahmed Tinubu ya raba wa Musulmi da Kirista da rikicin bayan zaben shekarar 2011 ya shafa tallafin Naira miliyan 10.
Wadanda suka amfana da tallafin kudin sun fito ne daga yankunan Musulmi da Kirista da ke Jihar Kaduna da suka rasa gidaje da dukiyoyinsu a lokacin wancan rikici.
Sanata Tinubu ya ce wannan kudi da ya bayar ya yi haka ne saboda tausaya wa wadanda rikicin ya shafa. Kuma ya bada taimakon ne a lokacin da jirgin yakin neman zaben Janar Muhammadu Buhari ya sauka a Kaduna.
Shi ma dan takarar Mataimakin Shugaban kasa na APC Farfesa Yemi Osinbajo ya raba wa mutanen kananan buhunan shinkafa.
Sanata Tinubu ya nemi mutane su ci gaba da addu’o’in neman zaman lafiya kuma su kauce wa duk wani abu da ka iya janyo rikici a lokacin zaben da za a a yi a watan gobe.
“Wannan taimako na Naira miliyan goma na bada shi ne kawai don kashin kaina ba daga asusun Jam’iyyar APC ba ne. Daga gare ni ne zuwa gare ku domin in rage muku radadin da kuke fama da shi. Amma ina rokonku da ku zabi APC, za ku zabi APC shin a shirye kuke ku zabi APC ba PDP ba, don Allah ku ce eh, za ku zabi APC,” inji shi.
Ya shawarci jama’a su tabbatar da sun kawar da mulkin PDP a Najeriya don samar da ci gaba mai ma’ana.
A jawabinsa, Farfesa Osinbajo kira ya yi ga jama’a da su kawar da bambancin da ke tsakaninsu domin samun zaman lafiya. A cewarsa APC ba jam’iyar addini ba ne kamar yadda wasu ke fadi.