Tinubu ya bai wa iyalan wadanda aka kashe a Katsina kyautar 100m

Masari ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su bari wani ya ribace su da maganar talauci da rashin tsaro.

Tinubu ya bai wa iyalan wadanda aka kashe a Katsina kyautar 100m

Gwamna Katsina, Aminu Bello Masari. (Hoto: Mobile Media Crew).

Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya bai wa iyalan wadanda ’yan bindiga suka kashe a jihar kyautar Naira miliyan 100.

Masari ya bayyana haka ne a taron yakin neman zaben Tinubu a Katsina, inda ya ce gwamnatinsa na kokarin kawo karshen matsalar rashin tsaro a jihar.

A cewarsa, dan takarar ya bayar da kyautar kudin don rabawa iyalan wadanda ’yan bindiga suka kashe sannan ya yi addu’ar Allah Ya jikan mutum 40 da ’yan bindiga suka kashe a jihar a makon da ya wuce.

Masari ya ce, “Shugabanci ba abun wasa ba ne, yana bukatar jajirtattun mutane; Idan ka yi wasa da shugabanci na lokaci kalilan, to za a shafe shekaru ana shan wahala.”

A cewarsa, da gwamnatocin baya sun yi abin da ya dace yanzu ba a samu ’yan ta’adda irin Boko Haram ba.

Don haka ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su yarda wani ya fake da matsalar talauci da rashin tsaro wajen neman kuri’arsu.