Tinubu ya bai wa mutanen da aka kai wa hari a coci tallafin N75m

Ya sanar da bai wa cocin tallafin Naira miliyan 25

Tinubu ya bai wa mutanen da aka kai wa hari a coci tallafin N75m

Mai neman takarar shugaban kasa jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ba da tallafin Naira miliyan 50 ga mutanen da harin da aka kai coci a garin Ondo na Jihar Ondo ya shafa.

Tinubu ya kuma bayar da tallafin Naira miliyan 25 ga cocin na St. Fransis da aka kai harin, wanda ya ce yankin Kudu maso Yammacin Najeriya bai taba ganin makamancinsa ba.

Ya sanar da haka ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje kan harin, ga Olowo na Owo, Oba Ajibade Gbadegesin  Ogunoye.

Ya kai ziyarar ta’aziyyar ce da rakiyar Gwamnan Jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, inda daga fadar basaraken ya je cocin domin gane wa kansa abin da ya faru.
Akalla mutum 30 ne aka kashe, yawancinsu mata da kanana yara, aka kuma jikkata wasu da dama, a harin da ’yan bindiga suka kai wa cocin a yayin da ake tsaka da ibada a safiyar ranar Lahadi.
Tinubu wanda ya je ta’aziyya a ranar Litinin ya bayyana harin da aka kai wa masu ibadar a matsayin shaidanci.
Ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dauki matakan magance matsalar tsaro, tare da alkawarin sannan ya yi alkawarin yin aiki tare da gwamnatin jihar domin tallafa wa mutanen da abin ya shafa.