Tinubu ya bayar da umarnin biyan tallafin man fetur – Rahoto
Wannan na zuwa ne biyo bayan zanga-zangar matsin rayuwa da aka yi a faɗin Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu, ya amince wa Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), da ya yi amfani da ribar shekarar 2023 da aka samu domin biyan tallafin man fetur.
TheCable ta ruwaito cewar shugaban ya kuma amince da dakatar da biyan riba da aka samu a 2024 ga gwamnati don taimakawa da kuɗaɗen da kamfanin zai kashe.
- NAJERIYA A YAU: Mece Ce Cutar Ƙyandar Biri Kuma Me Ke Jawo Ta?
- Cutar ƙyandar biri ba ta ɓulla a Gombe ba – Gwamna Inuwa
Ko da yake Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, sai dai akwai alamun da ke nuna cewar har yanzu gwamnati na kashe kuɗaɗe masu yawa a kan tallafin.
Sai dai, Gwamnatin Tarayya ta sha musanta biyan tallafin.
Idan ba a manta ba, ‘yan Najeriya sun yi zanga-zanga saboda wahalar da ake ciki a ƙasar, kuma ɗaya daga cikin buƙatunsu shi ne a dawo da tallafin man fetur.
Amma a cikin wani jawabin da Tinubu ya yi, ya bayyana cewa dawo da tallafin man fetur ba zai yiwu ba, inda ya bayyana cire tallafin a matsayin abu mai wahala amma kuma wajibi ne gwamnatinsa ta yi.
Ya ce tallafin ya kasance tamkar wata sarƙa da ta ɗaure tattalin arziƙin Najeriya.
A ranar Litinin, wata jarida a Intanet ta ruwaito cewa Tinubu ya amince wa NNPCL da ya biya tallafin bayan da kamfanin ya koka cewa ya yi amfani da duk hanyoyin da zai iya don samar da isasshen man fetur a ƙasar nan amma hakan ya gagara.
Ƙoƙarin ya haɗa da ƙara yawan samar da mai ta hanyar yaƙi da satar mai da lalata bututun mai; sake tsara bashi, jinkirta biyan ’yan kwangila, ’yan kasuwa da ayyukan da ba su da muhimmanci.
NNPCL y shaida wa shugaban cewa waɗannan ƙoƙarin sun gaza warware matsalar da ake fuskanta, kuma idan ba a biya tallafin ba, kamfanin ba zai iya sanya kuɗin da ake buƙata daga gare shi ga asusun Gwamnatin Tarayya ba.
Don haka, Tinubu ya umarci kamfanin da ya yi amfani da haraji da sauran kuɗaɗen da aka ware wa Gwamnatin Tarayya domin biyan kuɗaɗen tallafin man fetur.
Rahoton ya ce an bayar da wannan umarni ne a ranar 6 ga watan Yuni, 2024.
Hasashen da NNPCL ya yi, ya nuna cewa jimillar kuɗaɗen tallafin man fetur daga watan Agusta 2023 zuwa Disamban 2024 zai kai Naira tiriliyan 6.884, wanda zai hana kamfanin biyan Naira tiriliyan 3.987 na haraji da kuɗaɗen haƙƙin mai ga asusun Gwamnatin Tarayya.