Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta amince da naɗin sabon Babban Hafsan Sojin Ƙasa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta amince da naɗin Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ranar Juma’a. Tabbas akwai yunwa a Najeriya amma komai zai daidaita — Tinubu ’Yan bindiga sun sace […]

Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta amince da naɗin sabon Babban Hafsan Sojin Ƙasa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta amince da naɗin Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ranar Juma’a.

Onanuga ya ce matakin shugaban ya yi daidai da tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ya ce shugaban ƙasa ya tura wasika a hukumance zuwa Majalisar Dattawa domin tantancewa da tabbatar da sabon hafsan rundunar sojojin ƙasa.

“Shugaba Bola Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa wasiƙa yana neman a tabbatar da naɗin Laftanar Janar Olufemi Olatubosun Oluyede a matsayin Babban Hafsan Sojin Ƙasa (COAS).

“A wasikar da ya aike a yau [Juma’a], Tinubu ya nemi a tabbatar da naɗin Oluyede bisa tanadin sashe na 218 (2) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 da kuma sashe na 18 (1) na Dokar Sojoji.”

Ana iya tuna cewa, a ranar 30 ga watan Oktoba ne Tinubu ya naɗa Oluyede a matsayin muƙaddashin Babban Hafsan Sojin Ƙasa a sakamakon rashin lafiyar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

Amma daga bisani, Janar Lagbaja ya rasu a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2024.

A yanzu kuma Shugaba Tinubu ya buƙaci majalisa ta amince da naɗinsa a matsayin babban jami’in sojin ƙasa na Najeriya.

Ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa zai iya jan ragamar sojojin ƙasa wajen tabbatar da zaman lafiya a ƙasar nan.