Tinubu ya dakatar da Shugabar NSIPA, Halima Shehu
Shugaba Tinubu ya maye gurbinta har zuwa lokacin da za a kammala bincike
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Shugabar Hukumar Kula da Zuba Jari ta Kasa (NSIPA), Halima Shehu kan zargin almundahana.
Tinubu ya dakatar da ita ne a ranar Talata bayan zargin aikata zamba a hukumar sannan ya ba da umarnin za a gudanar cikakken bincike kan zargin da ake mata.
- NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Samun Kuɗi A 2024
- EFCC ta gayyaci tsohuwar ministar jin-kai kan badakalar 37bn
Shugaban kasar ya kuma da ba da umarnin maye gurbinta da Mista Akindele Egbuwalo a matsayin mukaddashin kodineta zuwa lokacin da za a kammala bincike.
Ya zuwa yanzu, shi ne mai kula da shirin na N-Power na kasa, kuma sabon nadin nasa zai fara aiki nan take.
Shugaba Tinubu ne ya nada Halima a watan Oktoban 2023, kuma Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin a ranar 18 ga watan Oktoba, 2023.