Tinubu ya damu game da harin Sakkwato – Minista
Ministan ya ce Tinubu ya damu matuƙa game da harin da ya yi sanadin mutuwar mutum 10 a jihar.
Gwamnatin Tarayya ta yi alƙawarin gudanar da cikakken bincike kan harbin bam da ya faru a ƙauyukan Gidan Bisa da Runtuwa a Ƙaramar Hukumar Silame, Jihar Sokoto, wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 10.
Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ne, ya bayyana hakan yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai wa Gwamnan Sakkwato, Ahmad Aliyu.
- Abba ya tarbi ɗaliban Kano 150 da suka kammala digiri na biyu a Indiya
- Bama-baman Lakurawa ne suka kashe mutane a Sakkwato – Sojoji
Yayin da yake magana a madadin Shugaba Bola Tinubu, ministan ya nuna damuwarsa kan lamarin kuma ya tabbatar da cewa za a yi adalci.
“Shugaban Ƙasa yana cikin damuwa game da wannan mummunan lamari, kuma ya aiko ni don na taya ku jaje,” in ji Matawalle.
Ya ƙara da cewa wani lokacin kuskure na iya faruwa yayin hare-haren jiragen sama saboda bayanan da aka samu ba daidai ba ne a lokacin aiwatar da ayyukan.
Ministan ya bayyana cewa yankin da aka harba bam ɗin na ƙarƙashin ikon Lakurawa.
“Rahotannin tsaro sun tabbatar da cewa al’ummar wannan yankin na ƙarƙashin ikon ‘yan ta’adda, wanda ya sa aka aiwatar da aikin,” in ji shi.
Gwamna Aliyu, ya yi kira ga sojojin su inganta tsarin tattara bayanai da sanya ido domin kaucewa irin wannan kuskure a nan gaba.
Ya kuma gode wa Shugaba Tinubu kan damuwarsa da kuma yaba wa sojoji da sauran hukumomin tsaro bisa jajircewarsu wajen tabbatar da tsaron jihar.
“Mun fahimci ƙalubalen da sojoji ke fuskanta, amma yana da muhimmanci a guji kuskuren da ke jawo asarar rayuka masu bin doka,” in ji gwamnan.
A halin yanzu, Hedikwatar Tsaro ta bayyana cewa bam ɗin da Lakurawa suka dasa ne ya yi sanadin mutuwar mutane 10.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, Janar Edward Buba, ya bayyana hakan.