Tinubu ya damu matuka da halin da ake ciki a Gabon – Ngelale
Ya ce zai tattauna da sauran shugabannin Afirka a kan batun
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya ce ya damu matuka da sabon juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Gabon.
Da sanyin safiyar Laraba ce dai sojojin kasar suka ayyana hambarar da gwamnatin Ali Bongo, sannan suka tsare shi a cikin gida.
- Mutumin da ya zana tutar Najeriya ya rasu
- Sojoji sun kama dan hambararren Shugaban Gabon kan zargin cin amanar kasa
Kasar Gabon dai ita ce ta baya-bayan nan da ta fuskanci juyin mulki a nahiyar Afirka. Ko a watan da ya wuce sai da sojoji suka kifar da gwamnatin Mohammed Bazoum na Jamhuriyar Nijar.
To sai dai a cewar mai magana da yawun Shugaba Tinubu, Ajuri Ngelale a yayin wani jawabi ga manema labarai a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja ranar Laraba, ya ce shugaban ya damu da halin da kasar ta fada.
Ajuri ya kuma ce Tinubu zai tattauna da sauran Shugabannin kasashe da ke Kungiyar Hadin Kan Afirka (AU) kan rikicin kasar da nufin lalubo bakin zaren.
Ya kuma ce, “Tinubu na nazarin abin da ya faru sosai, kuma ya damu matuka da halin da siyasar kasar ta ciki da kuma yadda kasashen Afirka ke yayin fadawa juyin mulki.
“Tinubu mutum ne da ya yi amanna da kare mulkin Dimokuradiyya, saboda ya yi imanin cewa mulki ya kamata ne ya zama a hannun jama’a, ba hannun masu karfi bindiga ba,” in ji Kakakin.
Kasar Gabon dai na da arzikin ma’adinai da dama, kuma ita ce kasa ta biyar a arzikin man fetur a nahiyar Afirka.
Kusan rabin arzikin kasar dai daga man fetur yake zuwa, sannan shi ne kusan kaso 80 cikin 100 na kayayyakin da take fitarwa ketare.