Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taron AU a Kenya

Shugaba Tinubu ya dawo ne bayan barin Abuja a ranar Asabar.

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taron AU a Kenya

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu a yammacin Litinin ya dawo Abuja daga birnin Nairobi na kasar Kenya.

Tinubu dai ya sauka ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, bayan ya halarci taron koli na tsakiyar shekara karo na 5 na Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta shirya.

Shugaban wanda ya halarci taron bahan halartar taron ECOWAS, ya bar Abuja ne tun a ranar Asabar.

A lokacin da yake birnin Nairobi, Shugaban ya bi sahun sauran shugabannin kasashen Afirka wajen tabbatar da hadin kai da gina nahiyar, tare da kokarin dakile duk wani rikici da ke neman kunno kai.

Ya kuma nuna aniyarsa ta karfafa rundunar ECOWAS da nufin dakile juyin mulki da yaki da ta’addanci a yankin.

Manyan jami’an gwamnati da dama ne suka tarbi Shugaban a filin jirgin saman, karkashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume da shugaban ma’aikatan fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila da Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodinnma, da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.