Tinubu ya dawo da tallafin mai
Gwamnatin Tinubu ta biya tallafin mai na N169.4bn a watan Agusta, duk da tabbacin da ya bayar cewa biyan tallafin ya zama tarihi
Duk da tabbacin da Shugaba Bola Tinubu ya sha bayarwa cewa tallafin man fetur ya zama tarihi, binciken Aminiya ya gano cewa Gwamnatin Tarayya ta kashe biliyan N169.4 a watan Agusta wajen biyan tallafin man.
Gwamnatin ta biyan kudaden ne domin tabbatar da ganin farashin litar man fetur din bai haura Naira 620.
- An cafke kwandasta kan zargin fyade a cikin mota
- NAJERIYA A YAU: Me Zai Faru Bayan Hukuncin Kotu Kan Zaɓen Kano?
Tun kafin yanzu, wasu na ganin cewa dawowar tallafin ya zama babu makawa, ganin yadda farashin litar man bai sauya ba, duk da cewa farashin gangar danyen mai a kasuwa duniya ya haura Dala 95.
Wata takarda da muka yi kicibus da ita a Hukumar Rabon Kudaden Gwamnati (FAAC) ua mima a watan Agusta, kamfanin gas na kasa (NLNG) ya biya Gwamnatin Tarayya ribar Dala Miliyan 275 ta hannun kamfanin NNPPC.
Daga cikin kudaden NNPC ya kashse Dala miliyan 220, kimanin Naira biliyan 169.4 wajen biyan tallafin man fetur, ya rike ragowar Dala miliyan 55, ba bisa ka’ida ba.
Takardar FAAC din ta nuna cewa an dawo da biyan tallafin mai kuma kamfanin NNPC na amfani da ribar da aka samu daga NLNG wajen biyan tallafin.