Tinubu ya fara jagoranci nagari — Buratai
Burutai ya ce akwai alamun ‘yan Najeriya su sake dawowa hayyacinsu karkashin mulkin shugaba Tinubu.
Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasan Najeriya (COAS), Lafkanar-Janar Tukur Buratai, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara aiki da kyau kuma ya dauko hanyar gyara.
Buratai, wanda kuma tsohon jakadan Najeriya ne a Jamhuriyar Benin, a cikin sakon taya murna na musamman na bikin ranar dimokuradiyya, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su mara wa shugaban kasa baya.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Zaben Shugabancin Majalisun Najeriya Zai Kasance
- Trump zai gurfana gaban kuliya kan boye bayanan sirri
“Shugaban kasa ya fara daukar hanya madaidaiciya. Don haka ya zama wajibi mu a matsayinmu na ’yan Najeriya mu mara masa baya don cimma burinsa.
“Tsayuwar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a kan tsarin dimokuradiyyar Najeriya, ina kyautata zaton za mu sake dawowa hanya madaidaiciya.
“Bari na kuma jinjinawa Cif MKO Abiola bisa sadaukarwar da ya yi na dimokuradiyya da muke ciki a yanzu. Wannan yana tabbatar da cewa sadaukarwarsa ba ta tafi a banza ba.
“Kishin kasa da hadin kai sun cancanci koyi daga dukkan shugabannin dimokuradiyya na kasa da kuma na duniya baki daya.
“Saboda haka, ina kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta ayyana ranar 12 ga watan Yuni a kowace shekara a matsayin ranar dimokuradiyya ta duniya.
“Wannan karramawa ce da ya kamata ake tunawa da Cif MKO Abiola ga duk masu son Dimokuradiyya daga kasashen duniya,” in ji Burutai.