Tinubu ya fi ƙarfin satar dukiyar Najeriya — Minista
Ministan ya ce Tinubu mutum ne mai arziƙin gaske, baya buƙatar azurta kansa da dukiyar Najeriya.
Ƙaramin Ministan Harkokin Matasa, Ayodele Olawande, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya fi ƙarfin ya saci dukiyar Najeriya.
Da yake jawabi a wajen taron Ƙungiyar Haɗin Kan Ma’aikata (JUNC), a Ma’aikatar Harkokin Ci Gaban Matasa a Abuja, Olawande, ya yi kira ga ‘yan Najeriya su ƙara haƙuri da halin da ake ciki a ƙasar nan.
- An Kama Shi Kan Kisan Dan Shekara 28 A Damaturu
- Aminu Dantata ya ba mutanen Maiduguri tallafin N1.5bn
Ya yi alƙawarin cewa nan ba da daɗewa ba za a ga sauye-sauyen da suka dace.
Ya bayyana cewa Tinubu mutum ne mai arziƙi, kuma ba shi da sha’awar satar dukiyar ƙasar nan.
“Tinubu ba talaka ba ne; ya jima da samun arziƙi, don haka ba shi da sha’awar satar dukiyar Najeriya,” in ji Olawande.
Ya kuma bayyana cewa shugabanci ba abu ne da zak dauwama ba, abin da ya fi muhimmanci shi ne irin gudunmawar da shugabanni suka bayar a lokacin da suke kan mulki.
Tinubu wanda ya yi gwamna har sau biyu kuma ya taɓa zama Sanata, yana da hannun jari da yawa a wurare da suka haɗa da gidaje, aikin jarida, da harkar shaƙatawa.
A wani taro kafin rantsar da Tinubu, uwargidansa, Oluremi Tinubu, ta ce iyalanta ba sa buƙatar dukiyar Najeriya don azurta kansu.
Ta yi alƙawarin cewa za su yi aiki domin inganta ƙasar nan don amfanin kowa da kowa.