Tinubu ya gana da Ganduje a Abuja

Ganawar dai ba ta rasa nasaba ba da ƙorafin da Ganduje yake da shi game da ganawar Tinubu da Kwankwaso a birnin Paris.

Tinubu ya gana da Ganduje a Abuja

Shugaban kasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, ya gana da Gwamnan Jihar Kano mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje a gidansa na Defense House da ke Abuja.

Da yammacin Asabar ɗin nan dai Ganduje ya shiga sahun waɗanda suka taro Asiwaju Tinubu lokacin da ya sauka Abuja daga ƙasar Faransa.

Bayan an isa gida kuma sun yi ganawar sirri tsakaninsu.

Ganawar dai ba ta rasa nasaba da ƙorafin da Ganduje yake da shi game da ganawar Asiwaju Tinubu da tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso a birnin Paris.

A baya-bayan nan dai aka ji wani sautin hirar wayar tarho na yawo inda Ganduje ke kukan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar bai kyauta masa ba da ya yi wannan tattaunawar.

Kawo yanzu dai Ganduje bai bayyana wa manema labarai matsayar da suka cimma da Asiwaju Tinubu ba.