Tinubu ya gana da gwamnoni kan kuncin rayuwa

Wannan shi ne taro na biyu da Tinubu ya yi da gwamnoni kan tattalin arziki.

Tinubu ya gana da gwamnoni kan kuncin rayuwa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya gana da gwamnonin jihohi 36 da ke fadin ƙasar a Fadar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja.

Taron na zuwa ne a matsayin wani yunkuri da gwamnati ke yi na rage tsadar kayan abinci da sauran kayayyakin masarufi.

Wannan dai shi ne karo na biyu da Tinubu ke ganawa da gwamnonin jihohin tun bayan da ya kaddamar da Majalisar Tattalin Arzikin Kasa a ranar 15 ga watan Yunin 2023.

Taron ba zai rasa nasaba da damuwar da ake nunawa a fadin kasar ba dangane da tsadar kayan abinci da rashin tsaro da sauran batutuwan da suka shafi tattalin arziki.

Daga cikin wadanda Aminiya ta hango a taron akwai Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima; Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume; Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun; Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila.

Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da; Abdulrahman Abdulrazaq; (Kwara) da Hope Uzodinma; (Imo); Farfesa Babagana Zulum (Borno); Godwin Obaseki (Edo) Sim Fubara (Ribas) Biodun Oyebanji (Ekiti) Charles Soludo (Anambra), Caleb Mutfwang (Filato) da Uba Sani (Kaduna) da sauransu.

A Larabar da ta gabata ce Majalisar Sarakunan Arewa ta yi koke dangane da matsi da kuncin rayuwa da al’ummar kasar ke fuskanta a dalilin tsadar kayan abinci baya ga matsalar tsaro.

Gwamnatin Tarayyar dai ta sha nanata cewa sauye-sauyen tattalin arziki da Tinubu ya yi ciki har da cire tallafin man fetur ya zama dole, inda ta kara da cewa wadannan matakan za su haifar da riba nan ba da jimawa ba.

Zanga-zanga ba za ta hana mu rusau a Abuja ba — Wike 

Lakurawa: Muna buƙatar taimakon Sakkwatawa — Hafsan Sojin Ƙasa

Mayakan Lukurawa sun kashe mutum 17 a Kebbi

Tsadar kayan abinci da rashin tsaro a Arewa abun damuwa ne —Sanata Babangida