Tinubu ya gana da gwamnonin Najeriya

Ganawar Tinubu ta farko da gwamnonin jihohi 36 da ke fadin Najeriya bayan hawansa mulki

Tinubu ya gana da gwamnonin Najeriya

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin jihohin kasar nan 36 karkashin kungiyar gwamnonin a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Wadanda suka halarci taron da aka fara da misalin karfe 12:36 na ranar Labada, sun hada da gwamnonin Zamfara da Kano da Taraba da Kogi da Ogun da Nasarawa da Bayelsa da Adamawa da  Ebonyi da kuma Legas.

Ragowar sun hada da Ribas da  Osun da Jigawa da Benuwai da Taraba da Delta da Enugu da Oyo da Filato da Kebbi da Abiya da Imo da kuma Jihar Bauchi.

Jihohin Edo da Neja ne kadai suka turo mataimakan gwamnoninsu domin wakiltarsu.

Gwamnonin da ba a fara taron da su ba sun hada da gwamnonin Katsina, Kaduna, Gombe, Borno, Kuros Riba, Akwa Ibom, Anambra, Ekiti, Sakkwato da kuma Ondo.

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, sun halarci zaman.

A ranar Juma’a ne Shugaba Tinubu ya gana da gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki.

A ranar Laraba ne dai Tinubu ya rantsar da Sanata George Akume a matsayin sakataren gwamnatin tarayya.