Tinubu ya gargadi sojin Nijar kan lafiyar Bazoum

Akwai yiwuwar za mu dauki matakin soji kan wadanda suka yi wa Bazoum juyin mulki.

Tinubu ya gargadi sojin Nijar kan lafiyar Bazoum

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya gargadi sojin da suka yi wa Mohamed Bazoum juyin mulki da su tabbatar rashin lafiyarsa ba ta ta’azzara ba yayin da suke ci gaba da yi masa daurin talala.

Cikin wata sanarwa da wani jami’in Turai ya fitar a wannan Juma’ar, Tinubu ya gargadi sojojin da su kwana da sanin cewa akwai “mummunan sakamako” idan suka kyale lafiyar hambararren shugaban ta ta’azzara.

A yayin wani kira da Shugaban Tarayyar Turai Charles Michel, Tinubu wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar ECOWAS da ke adawa da juyin mulkin Nijar, ya bayyana damuwarsa game da “tabarbarewar yanayin tsare shugaba Bazoum.”

A ranar 26 ga watan Yuli ne jami’an tsaron Fadar Shugaban Kasar Nijar suka tsare tsohon shugaban mai shekaru 63 tare da iyalansa, wanda ke zaman juyin mulki karo na biyar a kasar tun bayan samun ’yancin kai daga Faransa a shekarar 1960.

Tinubu ya jaddada kudirin ECOWAS da kuma manufofin siyasa na daukar mataki daya.

Duk da tasirin tattalin arzikin da wasu kasashen yankin ke fama da shi, ECOWAS za ta ci gaba da tabbatar da takunkumin, kamar yadda jami’in ya tabbatar.

Charles Michel ya jaddada cewa Tarayyar Turai za ta bai wa kungiyar ta ECOWAS cikakken goyon baya ba tare da kakkautawa ba, ya kuma yi Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a Nijar ba bisa ka’ida ba.

Ya kuma ce Tarayyar Turai ta ki amincewa da hukumomin da suka biyo bayan juyin mulkin tare da tabbatar da cewa shugaba Bazoum, wanda aka zaba bisa ka’ida, shi ne halastaccen Shugaban Nijar.

Za mu dauki matakin kan sojin Nijar — ECOWAS

Hafsoshin Tsaron Kungiyar Kasashen ECOWAS da ke kammala taronsu a wannan Juma’ar a birnin Accra na Ghana, na shirye-shiryen yiwuwar daukar matakin soji kan Jamhuriyar Nijar.

Bayanai sun ce hafsoshin sun amince da zaburar da sojojinsu na ko-ta-kwana a matsayin hanya daya tilo ta maido da mulkin dimokuradiyya a kasar.

Hafsoshin tsaron sun mayar da hankali kan daukar matakin soji domin maido da Bazoum kan kujerarsa muddin sojojin da suka yi juyin mulki suka ki amincewa da zaman sulhu.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta