Tinubu ya guji kurakuran da shugabannin baya suka yi — Abdulsalam

Abdulsalam ya ce shi kansa ya tafka kurakurai a baya.

Tinubu ya guji kurakuran da shugabannin baya suka yi — Abdulsalam

Tsohon Shugaban ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya shawarci shugaba Tinubu da ya yi taka-tsan-tsan da irin kurakuran da gwamnatocin baya suka yi wajen magance matsalolin Najeriya.

Ya ce hakan zai bai wa shugaba Tinubu damar tafiyar da gwamnatinsa tare da yin nasara.

Janar Abdulsalami wanda shi ne shugaban kwamitin zaman lafiya na ƙasa, ya bayyana haka ne a Abuja yayin wata hira da Sunday Sun.

Ya ce: “Kowane shugaba da ka sani, yana da kyawawan manufofinsa kuma yana rauni. Don haka dukkaninsu, zan iya cewa sun yi kokari kuma sun tafka kurakurai.

“Amma kamar yadda na fada, tsari ne na koyo. Ina fatan shugaban ƙasa Tinubu zai yi koyi daga kurakuran da shugabannin da suka tafka.

“Ba ina nufin cewa ban yi kuskure ba; tabbas, akwai kurakurai da yawa da na yi. Kowane shugaba ya yi kuskure.

“Ya kamata shugaban ƙasa mai ci ya duba tarihin ƙasar nan ya ga inda aka tafka kurakurai sannan ya yi ƙoƙarin gyara waɗannan kurakurai sannan kuma ya yi abin da yake ganin ya kamata wajen gudanar da mulkin ƙasar nan.”

Da yake ƙarin haske, tsohon shugaban ya ce bai yi nadamar miƙa mulki ga zaɓaɓɓiyar gwamnati a 1999 ba.

“Na yi farin ciki da abin da ke faruwa. Eh, ba komai ne yake daida ba, amma ga shi yau muna murnar cika shekara 25 na dimokuraɗiyyar da ba ta durƙushe ba,” in ji shi.

Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu

An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano

An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila

Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania