Tinubu ya halarci bikin rantsar da shugaba mafi ƙarancin shekaru a Afirka

Faye na ɗaya daga cikin ’yan siyasar adawa da aka saka daga kurkuku kwanaki 10 kafin gudanar da zaɓen.

Tinubu ya halarci bikin rantsar da shugaba mafi ƙarancin shekaru a Afirka

A wannan Talatar aka rantsar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin shugaban Senegal mafi ƙarancin shekaru.

Ɗan kishin Afirka mai shekara 44, ba a ƙasar Senegal kaɗai zai zama shugaba mafi ƙarancin shekaru ba, har ma a dukkan Afirka.

Shugabannin Afirka da dama ciki har da na Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, sun halarci bikin rantsar da shi a garin Diamniadio kusa da babban birnin Dakar.

A matsayinsa na shugaban kungiyar ECOWAS, shugaba Tinubu ya ce nasarar Bassirou Faye a zaben Senegal, wani ci gaba ne ga kungiyar a kokarinta na samar da zaman lafiya da tsarin mulki, tare da kara dankon zumunci tsakanin kasashe mambobin kungiyar.

Nan gaba kaɗan dai za a a yi bikin miƙa mulki a hukumance tare da Shugaba Macky Sall a fadar shugaban ƙasa da ke Dakar.

Faye na ɗaya daga cikin ’yan siyasar adawa da aka saka daga kurkuku kwanaki 10 kafin gudanar da zaɓen shugaban ƙasar a ranar 24 ga Maris.

Ya fita daga gidan yari bayan afuwar da Shugaba Macky Sall ya yi wa wasu fursunonin siyasa.

Ga wasu hotunan Tinubu da Bassirou Faye a yayin bikin rantsuwar.

Tinubu tare da Faye
Tinubu tare da wasu shugabannin Afirka a yayin rantsar da Bassirou Faye
Tinubu tare da Faye
Tinubu tare da wasu shugabannin Afirka a yayin rantsar da Bassirou Faye
Tinubu da Bassirou Faye

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos