Tinubu ya isa Brazil don halartar taron G20

Shugaba Bola Tinubu ya sauka a birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil domin halartar taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki (G20), wanda za a gudanar ranar Talata.

Tinubu ya isa Brazil don halartar taron G20

Shugaba Bola Tinubu ya sauka a birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil domin halartar taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki (G20), wanda za a gudanar ranar Talata.

Da misalin ƙarfe 3 na dare ne Tinubu da tawagarsa suka sauka a Brazil bayan sun baro Abuja.

Ministan harkokin wajen Brazil, Breno Costa ne ya tarbi Tinubu, ya samu rakiyar Mai Harkokin Wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar.

Sauran ’yan Tawagar Tinubu sun haɗa da Ministan Raya Al’adu da Yawo Buɗe Ido da Ƙirƙire-ƙirƙire, Hannatu Musawa da Ministan Kula da Dabbobi, Ido Mukhtar Maiha da sauransu.

A gabanin taron a birnin Rio de Janeiro, Shugaba Tinubu zai tattauna da wasu ƙasashe kan hanyoyin bunƙasa tattalin arziki.

Manufar taron ita ce lalubo hanyoyin inganta shugabanci da tattalin arziƙin ƙasashe da kuma muhalli.

 Shugaban Ƙasa Brazil, Mista Lula da Silva, zai karɓi baƙuncin taron G20 na 2024 ne a yayin da wa’adinsa na shugancin karɓa-karɓa na ƙungiyar yake ƙarewa a ranar 40 ga watan nan na Nuwamba. Ya karɓi ragamar shugabancin G20 ne a ranar 21 ga watan Disamba, 2023.

Tinubu zai halarci taron ne bisa gayyatar da ƙungiyar ta wa wakilai daga Ƙungiyar Tarayyar Afrika (AU) da Tarayyar Turai (EU).

Jakadan Brazil a Nijeriya, Mista Carlos Areias, Brazilian ne ya mika wa Shugaba Tinubu goron gayyatar daga Shugaba Da Silva’s a ranar 29 ga watan Agusta, lokacin da sabon Jakadan ya gabatar da takardar fara aikinsa ga Shugaba Tinubu a Abuja.

Mambobin Kungiyar G20 su ne; Argentina, Australia, Brazil, Kanada, China, Jamua, Faransa, Indiya da Indonesia.

Sauran su ne Italya Japan, Koriya ta Kudu, Meziko, Rasha, Saudiyya, Afirka ta Kudu, Turkiyya, Amurka da Birtaniya.

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano

Ya kamata a kori shugaban INEC —Obasanjo

Tinubu ya isa Brazil don halartar taron G20