Tinubu ya isa New York don halartar taron Majalisar Dinkin Duniya
Shugaba Tinubu zai gana da sauran shugabannin duniya a taron.
Shugaba Bola Tinubu ya isa filin jirgin sama na John F. Kennedy da ke birnin New York domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 (UNGA).
Shugaban ya isa filin jirgin da misalin karfe 7 na yamma agogon kasar, inda ya samu tarba daga ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar; Wakilin Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Farfesa Tijjani Muhammad-Bande da sauran jami’an gwamnati.
- Kotu ta tabbatar da Dauda Dare a matsayin Gwamnan Zamfara
- Za a fara kwato kuɗaɗe daga manoman da suka yi taurin bashi a Yobe
Taken taron UNGA na wannan shekara shi ne: “Sake Gina Hadin Kan Duniya: Habaka Aiki kan Ajandar 2030 da Manufofin Ci Gaba Mai Dorewa”.
A ranar 19 ga watan Satumba ne dai aka shirya shugaba Tinubu zai gabatar da jawabinsa na farko na kasa baki daya, wato ranar farko ta babbar muhawarar babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78.
Shugaba Tinubu zai shiga cikin jerin sauran shugabannin duniya da za su yi jawabi a taron.
Bugu da kari, shugaba Tinubu zai shiga babban taron tattaunawa kan samar da kudade don ci gaba; Babban Taro kan Rigakafin Cututtuka, zai tattauna da Babban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya da sauransu.