Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa a Fadar Gwamnatin Najeriya ta Villa da ke Abuja yau Alhamis, 14 ga watan Nuwamba. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila na daga cikin ƙusoshin gwamnati da suka halarci taron. HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja Zulum ya […]

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

Yadda aka yi taron Majalisar Zartarwa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa a Fadar Gwamnatin Najeriya ta Villa da ke Abuja yau Alhamis, 14 ga watan Nuwamba.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila na daga cikin ƙusoshin gwamnati da suka halarci taron.

Duk da babu wata sanarwa a hukumance amma ana hasashen taron wanda aka fara da misalin ƙarfe 1:11 na rana zai maida hankali ne kan shirye-shiryen Kasafin Kuɗin 2025.

Tinubu yayin jagorantar taron Majalisar Zartarwa

Wannan na zuwa ne mako guda bayan Shugaba Tinubu ya soke taron Majalisar Zartarwa da aka shirya gudanarwa a ranar Larabar makon jiya.

Tinubu ya ɗage taron ne sakamakon mutuwar Babban Hafsan Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

Sauran ƙusoshin gwamnati waɗanda aka hanga a taron sun haɗa da Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Misis Didi Walson-Jack da Wakilan sakataren gwamnati (SGF).

Yadda aka yi taron Majalisar Zartarwa

Aminiya ta ruwaito cewa kusan dukkan ministoci da sauran ’yan majalisar zartaswa sun halarci taron a wannan mako.

Ana hasashen dai taron FEC na yau na da alaƙa da shirye-shiryen kasafin kuɗin 2025 wanda Majalisar Tarayya ke dakon Shugaba Tinubu ya gabatar.