Tinubu ya janye nadin da ya yi wa matashi mai shekara 24 a shugabancin FERMA

Nadin matashin dai ya janyo ce-ce-ku-ce a fadin Najeriya

Tinubu ya janye nadin da ya yi wa matashi mai shekara 24 a shugabancin FERMA

Imam Kashim Imam

Shugaban Kasa Boa Tinubu, ya bayar da umarnin janye sunan Injiniya Imam Kashim Imam daga nadin da ya yi masa a matsayin shugaban Majalisar Daraktocin Hukumar Gyaran Hanyoyi ta Tarayya (FERMA).

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar da maraicen Alhamis.

“Umarnin janye sunan zai fara aiki ne nan take. Sai dai duk sauran nade-naden da aka yi na hukumar gudanarwar hukumar ta FERMA na nan daram,” in ji sanarwar.

Nadin matashin dai shekara 24 a makon da ya gabata ya janyo ce-ce-ku-ce matuka a fadin Najeriya.

Yayin da wasu suke jinjina masa kan nada matasa, wasu kuma sun soki lamirinsa kan nada wanda sam ba shi da wata kwarewa ya jagoranci hukumar.