Tinubu ya kai ziyarar jaje Maiduguri

Saukar Tinubu a garin Maiduguri ke da wuya ya zarce zuwa Fadar Shehun Borno

Tinubu ya kai ziyarar jaje Maiduguri

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Maiduguri domin jajanta wa al’ummar Jihar Borno bisa ibtila’in ambaliya da ta mamaye garin.

Saukar Tinubu a garin ke da wuya ya zarce tare da Gwamna Babagana Umara Zulum, zuwa Fadar Shehun Borno wanda shi ma ambaliyar ta mamaye fadar.

Tinubu wanda ya dawo Najeriya daga kasar waje ranar Lahadi zai gane wa idanunsa irin barnar da ambaliyar ta yi a Maiduguri.

Ana kuma sa ran zai samu ganawa da mutanen da abin ya shafa domin jajanta musu.

Tun da farko Tinubu ya tura Mataimakinsa, Kashim Shettima, wanda tsohon gwamnan jihar ne ya kai ziyarar jaje da gane wa idanunsa, inda a lokacin ya sanar da tallafin Naira biliyan uku daga Gwamnatin Tarayya.

Gwamna Zulum ya bayyana cewa sama da mutane miliyan daya ne ambaliyar ta shafa.

Ambaliyar wadda ita ce mafi muni cikin shekaru 30 a Maiduguri ta shafe kashi 70 na garin.

Hukumar Agajin Gaggawa tavaksa ta bayyana cewa iyalai 23,000 ne abin ya shafa, inda a halin yanzu wasunsu ke zaune a sansanin ’yan gudun hijira.

Ambaliyar wadda ta taso a sakamakon fashewar Madatsar Ruwa ta Alau, ta lalata manyan unguwanni da gadoji da hanyoyi da asibitoci da gine-ginen gwamnati da dama a Maiduguri.

Kazalika ta yi ajalin kashi 80 na namun daji da ke gidan zoo na Kyarimi.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja