Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Senegal Bassirou Faye

Bassirou Diomaye Faye shi ne Shugaban Kasa mafi ƙarancin shekaru a nahiyyar Afirka.

Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Senegal Bassirou Faye

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye a fadar Aso Rock da ke Abuja.

Wannan shi karo na farko da shugaban mafi ƙarancin shekaru a nahiyyar Afirka ya kawo ziyara Nijeriya tun bayan zamansa Shugaban Senegal a watan Afrilun da ya gabata.

Bayanai sun ce Bassirou Diomaye Faye mai shekaru 44 ya zo ziyarar aiki ne a Najeriya.

Sai dai zuwa babu masaniya a kan aikin da ya kawo Shugaban Senegal ɗin Najeriya.

Tinubu yana tarbar Bassirou Faye

A watan Afrilu da ya gabata ne aka rantsar Bassirou Diomaye Faye a matsayin shugaban Senegal.

An rantsar da ɗan jam’iyyar adawar bayan ya ni nasara da kashi 54 cikin ɗari na kuri’un da aka kaɗa a zaben a kan abokin hamayyarsa na hadakar jam’iyyu masu mulki.

Tinubu tare Bassirou Faye a fadar Aso Rock

Tinubu, wanda shi ne shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS), ya karɓi bakuncin Bassirou Faye tare da wasu ƙusoshin gwamnatin ƙasar.