Tinubu ya kori dukkan manyan hafsoshin tsaro

Ya kuma maye gurbinsu da sababbi na take

Tinubu ya kori dukkan manyan hafsoshin tsaro

Tsofaffin manyan Hafsoshin Tsaron Kasa

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kori dukkan manyan Hafsosin Tsaron Najeriya tare da maye gurbinsu da wasu sababbi.

Shugaban ya kuma daga likkafar Nuhu Ribadu zuwa matsayin mai ba shi shawara kan harkokin tsaron kasa (NSA).

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey ya fitar a daren Litinin.

Wadanda aka kora din su ne Babban Hafsan Tsaron na Kasa, Janar Lucky Irabor da Shugaban Sojojin Kasa, Farouk Yahaya da na Ruwa, Awwal Gambo da kuma na Sama, Isiaka Amao, sai kuma Babban Sufeton ’Yan Sanda na Kasa, Usman Alkali Baba.

Sabbin wadanda aka nada din dai su ne Manjo Janar C.G Musa a matsayin Babban Hafsan Tsaron Kasa da Manjo T. A Lagbaja a matsayin Shugaban Sojojin Kasa, sai Riya Admiral E. A Ogalla a matsayin Shugaban Sojojin Ruwa, sai AVM H.B Abubakar a matsayin Babban Hafsan Sojojin Sama.

Kazalika, Tinubu ya kori Manjo-Janar Babagana Monguno daga matsayin mai ba da shawara kan tsaron kasa, inda ya maye gurbinsa da Nuhu Ribadu.

Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne dai ya nada su a zamanin mulkinsa.