Tinubu ya manta da mu don ba mu da gwamnati —Ganduje
Ganduje ya koka kan ganawar da Tinubu ya yi da Kwankwaso a Faransa.
Ganawar zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da Sanata Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar NNPP na ci gaba da tayar da kura a tsakanin kusoshin jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Kano.
Aminiya ta ruwaito yadda Tinubu da Kwankwaso suka yi ganawar sa’o’i hudu a kasar Faransa, inda suka tattauna batutuwa da dama da suka hada da yiwuwar bai wa Kwankwaso mukami a gwamnatin Tinubu.
- Karin kudin tikiti: Za a dauki Dala 100 daga guzurin alhazai
- Sojoji sun ceto ma’aikaciyar agaji daga hannun ISWAP bayan shekara 4
Da yake mayar da martani, Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda, jigo a jam’iyyar APC a Kano, ya ce bai kamata Tinubu ya bai wa Kwankwaso wani mukami ba, ko da kuwa na dan aike ne.
“Mu a Arewa Maso Yamma ba ma maraba da Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jam’iyyarmu ta APC. Ba mu yarda da ra’ayin Bola Tinubu ya ba shi wani mukami ba ko da kuwa dan aike ne a jam’iyyarmu.
“Idan Tinubu ya yi watsi da kokenmu ya nada Kwankwaso, za mu hargitsa jam’iyyar APC a Arewa baki daya, mu janye goyon bayanmu gare shi,” in ji Kwamanda.
Jim kadan bayan Kwamanda ya yi wannan magana, wani sautin wayar tarho da aka nada tsakanin Ganduje da Ibrahim Masari, wanda tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APC ya karade gari.
A cikin faifan sautin, an ji gwamnan yana kukan rashin adalci da shugaban kasa ya yi masa a ganawarsa da Kwankwaso.
Ganduje ya ce duk da Masari ya shaida masa yiwuwar gudanar da irin wannan taron, amma babu wani abu da zai iya yi a kai.
“Amma a lokacin, da kun yi magana da shi (Tinubu). Kuna iya kiran sa ku yi magana da shi,” in ji Masari.
Sai aka ji gwamnan yana cewa “me zan iya fada masa? Yanzu shi (Tinubu) yana kallon Kwankwaso a matsayin mafita a gare mu? Ba matsala. Saboda ba mu da gwamnati? Kuma saboda shi (Tinubu) muka rasa gwamnati.
“Ko da zai gana da shi (Kwankwaso), kamata ya yi shi ma ya kira mu, ko da ba ta kai zuci ba.”
An kuma ji Masari, wanda na hannun daman Tinubu ne, yana kwantar wa da Ganduje hankali, yana kuma rokon sa da kada ya yi fushi har sai ya ziyarci Tinubu a ranar Alhamis ya ji ta bakinsa.
“Kuma duk wadannan abubuwan da suke faruwa daga Allah ne. Kuma lissafin da yake yi bai ma yi daidai ba… Shi kuma shi wannan mutumin, yaya ya kare da Jonathan?” in ji Ganduje.
Aminiya ta tattaro cewa gwamnan ya bar Kano zuwa Abuja da yammacin ranar Juma’a kuma da fatan zai gana da Masari a karshen mako, kafin tsohon gwamnan ya gana da zababben shugaban kasar, wanda zai dawo daga kasar waje nan gaba kadan.
Da aka tuntubi Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Abba Anwar, ya ce ba shi da hurumin yin magana a kan lamarin.
Duk da haka, bai musanta ko tabbatar da gaskiyar hirar ba. Wani bincike da Aminiya ta yi ta gano cewar sautin muryar da aka nada ba a yi masa coge ba.