Tinubu ya mayar da karin albashin da za a yi wa ma’aikata N35,000
Gwamnatin Tarayya ta kuma cire harajin man dizel daga yanzu zuwa watanni shida masu zuwa.
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi karin N10,000 kan karin N25,000 na wucin-gadi da za a yi wa albashin ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.
A safiyar wannan Lahadin ce Tinubu ya sanar da cewa ya amince da karin albashin 25,000 ga ƙananan ma’aikatan gwamnatin tarayya na tsawon wata shida.
- Liverpool ta sayar da wani bangare na hannun jarinta
- BUA ya rage farashin siminti zuwa N3,500 duk buhu
Tinubu ya sanar da haka ne a cikin jawabin da ya yi wa al’ummar Najeriya na ranar murnar cikar kasar shekara 63 da samun ’yancin kai.
Sai dai a wata sanarwa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila ya fitar, ya ce an yi karin N10,000 kan karin N25,000 da Shugaban Kasar ya sanar a baya.
Haka kuma, sanarwar ta ce karin albashin zai shafi dukkan ma’aikata sabanin sanarwar farko da ce zai ta’allaka ne kadai a kan kananan ma’aikata.
Aminiya ta ruwaito cewa, wannan lamari dai na zuwa ne bayan zaman sulhu da Gwamnatin Tarayya ta yi tare da kungiyar ’yan kwadago da ke shirin tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a ranar Talata.
Bayanai sun ce, a yayin taron na gaggawa da Gwamnatin Tarayyar ta kira a Yammacin wannan Lahadin, shugabannin ƙungiyar ƙwadagon sun bayyana rashin gamsuwar da tayin karin albashin N25,000 da aka yi karon fari.
Ana iya tuna cewa, Tinubu wanda a cikin jawabin nasa ya ce yana sane da halin tsanani da al’umma suka faɗa sanadiyyar matakan da gwamnatinsa ke ɗauka, ya ce wajibi ne ’yan Najeriya su jure hali na tsanani matukar suna son ganin ƙasar ta samu ci gaba.
Gwamnati ta cire harajin man dizel
Kazalika, a yunkurin da Gwamnatin Tarayyar take yi don ganin ta rage wa ’yan Najeriya radadi, ta sanar da cire harajin da ake biya a kan man dizel.
Shi ma dai cire harajin na VAT gwamnatin ta ce na wucin-gadi ne nan da watanni shida a ƙoƙarin da take yi na ganin ƙungiyar ƙwadago ba ta tsayar da al’amura a kasar ba.
Wannan jawabi na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ministan Labarai da Wayar Kan ’Yan Kasa, Mohammed Idris ya fitar.
Ministan ya ce cire harajin man na dizel wata matsaya ce da Gwamnatin Tarayya ta cimma yayin ganawarta da shugabannin ƙungiyar ƙwadagon na NLC da TUC a Fadar Shugaban Kasa.