Tinubu ya mika kudurin karin albashi zuwa N70,000 ga Majalisa
Shugaba Tinubu ya mika kudurin karin mafi karancin albashi zuwa N70,000 ga Majalisa
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika kudurin karin mafi karancin albashi zuwa N70,000 ga Majalisar Dokoki ta Kasa.
A ranar Talata shugaban ya mika kudurin karin albashin domin amincewar majalisa dokokin kasa kafin ya zama doka a fara biyan albashin.
Shugaban kasar ya bukaci majalisar ta hanzarta amincewa da kudurin na karin albashi, domin zama doka da kuma aiwatarwa.
Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da takwaransa na Majalisar Wakilai Abbas sun samu wasikar kudurin da ke neman amincewar mambobin majalisun.
- ’Yan ta’adda sun fara amfani da jirgi mara matuki —ONSA
- Sheikh Tijjani Guruntum ya gwangwaje dalibansa da kyautar kuɗi da kayan abinci
N70,o00 shi ne mafi karancin albashin da shugaban kasar da kugniyoyin kwadago suka amince a kara daga Naira 30,000, bisa sharadin za a rika karawa bayan duk shekaru uku.
Shugaban kasan ya kuma aike wa majalisar da bukatar yin gyara ga dokar aikin dan sanda domin dacewa da Sashe na 58 na kudin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa gyaran fuska.