Tinubu ya naɗa ɗan Ganduje darakta a Hukumar Lantarki ta REA

Ana zargin daraktocin da aka dakatar da karkatar da dukiyar hukumar ta fiye da naira biliyan 1.2

Tinubu ya naɗa ɗan Ganduje darakta a Hukumar Lantarki ta REA

Umar Abdullahi Umar tare da mahaifinsa, Abdullahi Umar Ganduje

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Umar Abdullahi Umar, ɗan tsohon Gwamnan Kano kuma Shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin ɗaya daga cikin manyan daraktocin Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA).

Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban kasar ya dakatar da shugaban hukumar, Ahmad Salihijo Ahmad.

Dakatarwar ta sai abin da hali ya yi ta kuma haɗa da wasu manyan daraktoci uku na hukumar kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya fitar ta nuna.

Sanarwar da Mista Ngelale ya fitar a yammacin wannan Alhamis ɗin, ta ce sauran manyan jami’an hukumar uku da dakatarwar ta shafa sun haɗa da Olaniyi Alaba Netufo da Barka Sajou da Sa’adatu Balgore.

Tinubu ya kuma bayar da umarnin gudanar da bincike kan jami’an dangane da zargin karkatar da dukiyar hukumar ta fiye da naira biliyan 1.2 a ɗan tsukukun shekaru biyu da suka gabata.

Bayanai sun ce hukumomin yaƙi da rashawa sun soma tatso wani kaso daga cikin kuɗin da ake zargin manyan jami’an sun yi ruf da ciki a kai.

Tuni dai shugaban kasar ya maye gurbinsu da sabbin shugabanni da suka haɗa da Abba Abubakar Aliyu a matsayin Manajan Darakta na hukumar ta REA.

Sauran waɗanda shugaban kasar ya naɗa a matsayin manyan daraktocin da za su maye gurbin waɗanda ya dakatar sun haɗa da Ayoade Gboyega da Umar Abdullahi Umar da Doris Uboh da kuma Olufemi Akinyelure a matsayin shugaban sashen kula da manyan ayyukana hukumar.

Ngelale ya ambato shugaban kasar na cewa ana kyautata zaton dukkan wadanda aka yi wa sabbin nadin za su sauke nauyin da rataya a wuyansu cikin gaskiya da rikon amana.

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki a Gaza

Isra’ila ta sake fitar da sabon sharaɗin tsagaita wuta a Gaza

Mutanen da gobarar tankar mai ta kashe sun kai 86 a Neja

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun