Tinubu ya naɗa Ali Nuhu Shugaban Hukumar Fina-Finai ta Kasa

Ali Nuhu na cikin jerin wadanda Tinubu ya nada a hukumomin da ke karkashin Ma’aikatar Al’adu ta Tarayya.

Tinubu ya naɗa Ali Nuhu Shugaban Hukumar Fina-Finai ta Kasa

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa jarumin Kannywood, Ali Nuhu a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Shirya Fina-Finai ta Najeriya.

Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya fitar a wannan Juma’ar.

Ali Nuhu wanda fitaccen jarumi ne a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, na daga cikin jerin wadanda shugaban kasar ya nada a hukumomin daban-daban da ke karkashin Ma’aikatar Al’adu ta Tarayya.

Sauran wadanda nadin mukaman ya shafa sun hada da: Tola Akerele da Shaibu Husseini da Obi Asika da Aisha Adamu Augie da kuma Ekpolador-Ebi Koinyan.

Akwai kuma Ahmed Sodangi da Chaliya Shagaya da Hajiya Khaltume Bulama Gana da Biodun Ajiboye da kuma Ramatu Abonbo Mohammed.