Tinubu ya naɗa Babatunde Ogunjimi Akanta Janar na Tarayya

Naɗin nasa, wanda aka amince da shi a yau Talata, zai fara aiki ne daga ranar 7 ga Maris 2025, ranar da Oluwatoyin Madehin za ta yi ritaya.

Tinubu ya naɗa Babatunde Ogunjimi Akanta Janar na Tarayya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Shamsedeen Babatunde Ogunjimi a matsayin sabon Akanta Janar na Tarayya.

Naɗin nasa, wanda aka amince da shi a yau Talata, zai fara aiki ne daga ranar 7 ga Maris 2025, ranar da Oluwatoyin Madehin za ta yi ritaya.

Ana iya tuna cewa, tun a watan Disambar da ya gabata ne aka bayyana Ogunjimi mai shekaru 57 a matsayin magajin Madehin.

Daga baya aka naɗa wani kwamitin ƙwararru da zai tantance shi wanda ya ƙunshi manyan daraktocin daga a ma’aikatun gwamnatin tarayya daban-daban.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce kwamitin ya yi tantancewar bisa matakai uku masu tsauri da suka haɗa da a rubuce, gwajin ƙwarewar fasahar sadarwar da kuma hira ta baka.

Ogunjimi ya kammala karatunsa na digiri a Jami’ar Nijeriya, Nsukka, a shekarar 1990, inda ya sami digiri na farko a fannin lissafin kuɗi.

Ya kuma samu wani digiri na biyun a wannan fannin a Jami’ar Legas.

Kazalika, sabon Akanta Janar ɗin mamba ne a Cibiyar Akantoci na Nijeriya da Cibiyar Haraji ta Nijeriya.

Sanarwar ta ƙara da cewa, Shugaba Tinubu ya taya Ogunjimi murna, ya kuma buƙaci da ya hidimta wa Nijeriya bisa gaskiya, ƙwarewa, da sadaukarwa.