Tinubu ya naɗa Ministan Kiwon Dabbobi bayan sallamar wasu 5

Tinubu ya naɗa minista a sabuwar ma’aikatar bunkasa kiwon dabbobi da matar Ojukwu a majalisar ministocinsa

Tinubu ya naɗa Ministan Kiwon Dabbobi bayan sallamar wasu 5

Shugaba Tinubu ya naɗa Ministan Bunƙasa Kiwon Dabbobi, makonnni kaɗan bayan ya karɓi rahoton Kwamitin Shugaban Ƙasa kan kafa ma’aikatar.

Shugaban ƙasan ya kuma sanar da naɗi Idi Mukhtar Maiha a matsayin ministan sabuwar ma’aikatar.

Naɗin ministan kula bunkasa kiwon dabbobin na cikin jerin sabbin ministoci bakwai da shugaban ƙasan ya naɗa bayan sallamar wasu ministoci daga gwmanatinsa.

Sabbin ministocin nasa sun haɗa da maza huɗu da mata uku, ciki har da Ambasada Bianca, matar tsohon madugun neman kafa ƙasar Biafra, Marigayi Odumegwu Ojukwu, a matsayin Ƙaramar Ministar Harkokin Waje.

Mace ta biyu ita ce Dokta Suwaiba Sa’id Ahmad a matsayin Ƙaramar Ministar Ilimi sai Jumoke Oduwole a matsayin Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari.

Kafin yanzu, Jumoke Oduwole, ita ce Babbar Sakatariyar Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Samar da Kyakkyawan Yanayi domin Kasuwanci.

Sauran ministocin sun haɗa da Muhammad Maigari Dingyaɗi, tsohon Ministan Harkokin ’Yan Sanda a zamanin Buhari, a matsayin sabon Ministan Ƙwadago.

Yusuf Abdullahi Ata shi ne sabon Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane sai Yilwatda.

A ranar Laraba ne Tinubu ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul inda ya sallami ministocin biyar, ya naɗa bakwai sabbi, ya sauya wa 10 wuraren aiki tare da daga likafar kananan ministoci 10.

Kazalika shugaban kasan ya naɗa tsohon dan jarida kuma tsohon Ministan Wasanni, Sunday Dare, a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin haulɗa da jama’a.

Daga cikin waɗanda Tinubu ya sallama daga majalisar ministocinsa, har da Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, wanda yanzu ƙaramin ministan ma’aikatar, Morufu Alausa, ya maye gurbinsa.

Ita ma Ministar Harkokin Mata, Uju Kennedy-Ohaneye an sallame ta, aka maye gurbinta da Imam Sulaiman Ibrahim, tsohuwar Ƙaramar Ministar Harkokin ’Yan Sanda.

Shi kuma Ƙaramin Ministan Matasa, Ayodele Olawenda, an ɗaga likafarsa zuwa babban ministan ma’aikatar.

Ana iya tuna cewa a ranar Laraba da shugaban kasa ya yi waɗannan naɗe-naɗen ne ya rushe ma’aikatun tarayya guda hudu.

A lokacin da yake karɓar baƙuncin Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF), ya yi alƙawarin sallamar ministocin da ba su taɓukawa.

Waɗanda aka rushe su ne ma’aikatar Wasanni ta Ƙasa da Ma’aikatar bunkasa yankuna, waɗanda yanzu za su koma ƙarƙashin sabuwar ma’aikatar bunkasa ci-gaban yankuna ta ƙasa.

Ita kuma ma’aikatar Wasanni da aka rushe ayyukanta za su koma hannun ƙarƙashin Hukumar Bubƙasa Wasanni ta Ƙasa.