Tinubu ya naɗa sabbin shugabannin NIA da DSS

Tinubu ya ce yana sa ran sabbin shugabannin hukumomin su yi aiki cikin ƙwarewa.

Tinubu ya naɗa sabbin shugabannin NIA da DSS

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, naɗa sabbin shugabannin Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Ƙasa (NIA) da Hukumar Tsaro ta DSS.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale je, ya bayyana haka a yammacin ranar Litinin.

Ya ce an naɗa Ambasada Mohammed Mohammed a matsayin sabon Darakta-Janar na hukumar NIA.

Har wa yau, Tinubu ya naɗa Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin sabon Drakta-Janar hukumar tsaro ta DSS.

Wannan ya biyo bayan murabus da Yusuf Bichi ya yi daga muƙaminsa na shugaban DSS.

Ngelale, ya bayyana cewa Ambasada Mohammed ya samu nasara a aikinsa tun bayan shiga NIA a shekarar 1995.

Ya riƙe mukamai daban-daban har zuwa matakin darakta, sannan aka naɗa shi shugaban ofishin Jakadancin Najeriya a Libiya.

Ambasada Mohammed ya kammala karatunsa a Jami’ar Bayero ta Kano, a shekarar 1990, kuma ya yi aiki a ƙasashe irin su Koriya ta Arewa, Pakistan, Sudan da kuma a Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja.

Sabon Darakta-Janar na DSS, Adeola Ajayi, ya samu nasara har zuwa matsayin mataimakin Darakta-Janar.

Ya kuma yi aiki a matsayin daraktan jiha a Bauchi, Enugu, Bayelsa, Ribas, da kum Jihar Kogi.

Ngelale, ya ƙara da cewa waɗannan naɗe-naɗen sun biyo bayan saukar tsofaffin shugabannin NIA da DSS.

Shugaba Tinubu yana sa ran sabbin shugabannin za su nuna ƙwarewar aiki a waɗannan hukumomi wajen magance matsalolin tsaro ta hanyar yin aiki tare da sauran hukumomi da kuma Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA).

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur