Tinubu ya naɗa sabon shugaban Hukumar gidan gyaran hali ta Nijeriya

Naɗin nasa ya biyo bayan ƙarewar wa’adin Shugaban Hukumar na yanzu, Haliru Nababa.

Tinubu ya naɗa sabon shugaban Hukumar gidan gyaran hali ta Nijeriya

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Nwakuche Ndidi a matsayin muƙaddashin Konturola-Janar na Hukumar da ke lura da gidajen gyaran hali ta Nijeriya. 

Naɗin nasa ya biyo bayan ƙarewar wa’adin Shugaban Hukumar na yanzu, Haliru Nababa.

Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya naɗa Nababa a ranar 18 ga Fabrairu, 2021.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, Sakataren Hukumar sibil defens, Hukumahr gyaran hali, Hukumar kashe gobara da Hukumar Shige da Fice ta ƙasa, Ja’afaru Ahmed, ya ce naɗin Ndidi zai fara aiki ne daga ranar 15 ga Disamba, 2024.

Ahmed ya ci gaba da cewa, “Shugaban ƙasa kuma babban kwamandan sojojin ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya amince da naɗin Nwakuche Sylɓester Ndidi a matsayin muƙaddashin shugaban Hukumar da ke lura da gidajen gyaran hali ta Nijeriya, bayan ƙarewar wa’adin Haliru Nababa. Naɗin nasa dai zai fara aiki daga ranar 15 ga Disamba, 2024.

“Nwakuche, wanda aka haifa a ranar 26 ga Nuwamba, 1966, ɗan asalin garin Oguta a Jihar Imo. Har zuwa lokacin da aka naɗa shi, ya kasance Mataimakin Kwanturola-Janar mai kula da Hukumar Horo da Ci gaban Ma’aikata.

’Yan sanda sun kama baƙin haure 165 a Kebbi

Gobara ta yi ajalin almajirai 17 a Zamfara

Saura ƙiris Bello Turji ya zo hannu – Ministan Tsaro

Sarkin Jiwa a Abuja ya yi rashin mahaifiya