Tinubu ya naɗa sabuwar Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya
Didi Esther Walson-Jack za ta maye gurbin Folashade Yemi-Esan wadda za ta yi ritaya a watan Augusta.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Misis Didi Esther Walson-Jack OON a matsayin sabuwar Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.
Naɗin kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ya fitar a Yammacin wannan Larabar ta ce zai fara aiki ne daga ranar 14 ga watan Agustan 2024.
- Ina roƙon ’yan Nijeriya da su ƙauracewa shiga zanga-zanga — Zulum
- Tinubu zai ƙara fiye da N6trn a Kasafin Kuɗin 2024
A shekarar 2017 ne aka naɗa Misis Walson-Jack a matsayin Babbar Sakatariya inda ta yi aiki a ma’aikatu daban-daban.
Sabuwar shugabar ma’aikatan za ta maye gurbin Dokta Folashade Yemi-Esan wadda za ta yi riyaya a ranar 13 ga watan Agustan bana.
Yayin da yake yi wa Dokta Yemi-Esan godiya dangane da ƙoƙarin da ta yi wajen gudanar da aiki, Tinubu ya kuma buƙaci sabuwar shugabar ma’aikatan da jajirce wajen sauke nauyin da rataya a wuyanta tare da riƙo da gaskiya da kiyaye dokokin aiki.