Tinubu ya nada dan Arewa Sakataren Gwamnati

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jigawa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, ya zama Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa.

Tinubu ya nada dan Arewa Sakataren Gwamnati

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada tsohon Gwamnan Jihar Binuwai kuma tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Sanata George Akume a matsayin sakataren Gwamnati.

Sanarwar da Daraktan Yada Labaran Fadar Shugaban Kasa, Abiodun Oladunjoye, ya fitar a ranar Juma’a ta ce a ranar kuma Shugaba Tinubu ya nada Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa.

“Shugaba Tinubu ya kuma nada tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, a matsayin Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa.

“A lokacin ganawarsa da Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyarsa ta APC, Shugaba Tinubu ya kuma nada tsohon Gwamnan Binuwai kuma tsohon Ministan Ayyuka na Musamman a Gwamnatin Buhari, Sanata George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya.”

Sanarwar na zuwa ne bayan a ranar Alhamis gari ya dau zafi da rade-radin cewa Tinubu ya nada Gbajabiamila a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa.

Gwamnonin Jam’iyyar APC mai mulki da suka halarci taron sun samu jagorancin shugabansu kungiyarsu kuma Gwamnan Imo, Hope Uzodinma.

Sai Gwamna Babagana Zulum (Borno), da Mai Mala Buni (Yobe), Babajide Sanwo-Olu (Legas), Yahaya Bello (Kogi), Abdullahi Sule (Nasarawa), Umar Namadi (Jigawa), Inuwa Yahaya (Gombe), wadanda suka fara wa’adin mulkinsu na biyu.

Sauran su ne AbdulRahman AbdulRazaq (Kwara), Dapo Abiodun (Ogun).

Sai kuma gwamnonin da suka fara wa’adinsu na farko, Uba Sani (Kaduna), Dikko Radda (Katsina), Rabaran Hyacinth Alia (Binuwai), Umar Bago (Neja), Aliyu Ahmed (Sakkwato), Francis Nwifuru (Ebonyi) da kuma Bassey Otu (Kuri’a Riba)

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba