Tinubu ya nada Jalal Ahmad a matsayin sabon Shugaban NAHCON

Nadin zai zama na tsawon shekaru huɗu ne

Tinubu ya nada Jalal Ahmad a matsayin sabon Shugaban NAHCON

Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), Jalal Ahmad

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya nada Alhaji Jalal Ahmad a matsayin sabon Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON).

Mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da maraicen Talata.

Sanarwar ta kuma ce tuni Shugaba Tinubu ya bukaci Shugaban hukumar ma barin gado, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, da ya tafi hutun shirye-shiryen barin aiki na wata uku kamar yadda dokar aikin gwamnati ta tanada.

“Zai fara hutun ne daga ranar 18 ga watan Oktoba, 2023, kafin ya yi ritaya ranar 17 ga watan Janairun 2023.

“Sabon shugaban zai fara aiki ne a matsayin rikon kwarya daga ranar 18 ga watan na Oktoba, sannan ya fara cikakken wa’adin shekara hudu daga ranar 17 ga watan Janairun 2023.

“Bugu da kari, Tinubu ya amince da rushe hukumar gudanarwar hukumar ta NAHCON.

“Shugaban yana kuma sa ran sabon shugaban zai gudanar da aikinsa da tsoron Allah, sannan ya yi shi yadda Alkur’ani ya koyar,” in ji sanarwar.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna