Muhimman abubuwa 5 kan sabon shugaban EFCC Ola Olukoyede
Sakataren EFFC, Ola Olukoyede ya zama sabon shugabanta, Muhammad Hassan Hammajoda kuma ya zama sakatare
Tsohon Sakataren Hukumar Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tatttalin Arziki Ta’annati (EFCC) a matsayin sabon shugabanta.
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Olukoyede ne tare da Muhammad Hassan Hammajoda a matsayi sabodan Sakataren EFCC.
Abubuwa 5 Wane sabon shugaban EFCC?
- Ola Olukoyede kwararre ne a fannin tabbatar da bin ka’ida, hana almundahana, da kuma bincikar kamfanoni.
- Barista Ola Olukoyede kwararren mai binciken kwakwaf ne kuma lauya ne na tsawon shekara 22.
- Mamba ne a kwamitin gwamnatin tarayya kan gyaran sashen binciken kudade ta kasa (NFIU).
- Shi ne shugaban ma’aikatan shugaban EFCC daga 2016 zuwa 2018, skearar ya zama sakataren hukumar.
- A ranar Alhamsi 12 ga watan Oktoba, 2023 aka nada shi shugaban hukumar a wa’adin farko na shekara hudu.
- Dan asalin kabilar Ikere-Ekiti ne daga Jihar Ekiti, kuma an haife shi ranar 4 ga Oktoba, 1969.
Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa shugaban kasar ya nada Olukoyede ne bayan tsohon mukaddashin shugaban EFCC da aka dakatar, Abdulrasheed Bawa ya ajiye aiki.
sanarwar nadin Olukoyede da kakakin shugaban kasa Ajuri Ngelale ya fitar ta ce Misata Olukoyede ya cika duk ka’idoji da kuma cancantar jagorantar hukumar bayan ajiye aikin da Abdulrasheed Bawa ya yi, sai dai ba ta yi karin bayani ba.
Nadin Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukumar zai tabbata ne bayan amincewar Majalisar Dattawa.
Shugabanni EFFC biyu da suka gabaci Olukoyede, Abdulrasheed Bawa da kuma Ibrahim Magu, ba su samu amincewar majalisar ba, har zuwa lokacin da aka dakatar da su kan zargin almundahana, aka maye gurbinsu.