Tinubu ya nada sabbin shugabannin NTA, NAN da NBC
Hukumomi takwas ne aka yi wa nade-naden
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi sabbin nade-nade a hukumomin gwamnatin Tarayya guda takwas da ke karkashin Ma’aikatar Yada Labarai da Wawar da Kan Jama’a ta kasa.
Kakakin Shugaban, Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da yammacin Alhamis.
- An dakatar da shugaban APC na Karamar Hukuma a Jigawa kan zargin yi wa ’yar aikin gidansa fyade
- ’Yan bindiga sun kai hari gidan yarin Kalaba
Wadanda ya nada din su ne Lanre Issa-Onilu a matsayin shugaban Hukumar Wayar da kan Jama’a ta Kasa (NOA), sai Salihu Abdulhamid Dembos da aka nada shugaban Hukumar Gidan Talabijin na Kasa (NTA).
Sauran wadanda aka nada din su ne Dokta Muhammed Bulama a matsayin sabon shugaban Hukumar Gidajen Rediyon Tarayya ta Najeriya (FRCN) da Charles Ebuebu a matsayin shugaban Hukumar Kula da Kafafen Yada Labarai ta Kasa (NBC) da Jibrin Baba Ndace a matsayin shugaban Muryar Najeriya (VON).
Sanarwar ta kuma ce, “Shugaba Tinubu ya kuma nada Dokta Lekan Fadolapo a matsayin shugaban Hukumar Kula da Tallace-tallace ta Najeriya (ARCON) da Ali Muhammad Ali a matsayin shugaban Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) yayin da Dili Ezughah zai zama sabon Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Jaridu ta Kasa (NPC).
“Shugaban ya hore su da su yi amfani da kwarewarsu wajen fito da nagartattun hanyoyin da za su bunkasa ci gaban Najeriya ta hukumomin da aka dora musu jagorancinsu.
“A sakamakon wannan sanarwar, wadannan nade-naden sun fara aiki ne nan take,” in ji Ajuri Ngelale.